Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jonathan ta Mayarda Martani Kan Buhari


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, 11 ga Disamba 2014.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, 11 ga Disamba 2014.

Gwamnatin shugaba Jonathan ta mayarda martani kan sake tsayar da Janaral Buhari tsayawa zaben shugaban kasa karo na hudu.

Mai baiwa shugaban kasa shawara ta fuskar siyasa Farfasa Rufai Ahmed Alkali yace sun san hanyar kayar da Buharin.

Abun da jam'iyyar APC tayi yayi kyau sabili da su a PDP sun san Buhari. An yi zabuka uku can baya duk ya fadi sabili da haka dole su san irin kamun ludayinsa. Tsayar da Buharin zai kawo masu saukin siyasa nan gaba.

Amma ya roki jama'arsu wai su yi hattara domin suna son a samu sauki lokacin siyasa din da kuma bayanta, wato lokacin zabe da bayan zabe kada a samu tashin hankali. Kada mutane su yi anfani da sunan shugaban kasa ko shi Buharin suna munanan kalamai da ka iya kawo hargitsi.

Shugaba Jonathan baya son a kashe kowa a rayuwarsa ko sabili dashi ko kuma sabili da abun da yake nema. Akan ko bangaren Jonatahn sun firgita sabili da dimbin magoya baya da Buhari yake dasu sai Farfasa yace ai shi ma Jonathan yana da magoya baya a duk fadin Najeriya.

A bangaren adawa ana samun banbancin ra'ayi tsakanin masu marawa Buhari baya da masu ganin da an samu sauyi a wannan karon zai fi tasiri wajen tunkarar PDP.

Sale Bakoro Sabon Fegi Damaturu yana murna da nasarar Buhari. Yace yana murna musamman domin suna fama da rashinkwanciyar hankali a arewa. A mulkin PDP ne aka samu dubban masu gudun hijira. Sabili da haka ya kira 'yan Najeriya su taru su marawa Janaral Buhari baya domin ya ci zabe, ya kwato kasar daga kangin da ta shiga.

Amma Umar Abdullahi Agyewa Alago yana cizon yatsa. Yana fatan da Atiku ne ya lashe zaben. Injishi Atiku ne kawai zai iya takurar da gwamnatin PDP.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG