Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Shugaba Obama ta kai karar jihar Carolina ta Arewa Kotu


Loretta Lynch, antoni janar din Amurka
Loretta Lynch, antoni janar din Amurka

Gwamantin shugaba Barack Obama ta kai karar jihar Carolina ta Arewa game da dokar jihar ta bambanta ban dakin maza ko matan da aka haifa da al’aurar mata da na maza, amma daga baya suka zabi a maida su jinsi daya.

Wanda suka ce dokar ta sabawa dokar gwamnatin tarayya game da hana tsangwama. Wacce dokar tace, idan mace ta sa aka rikida halittarta zuwa namiji, ko aka rikida halittar namiji ya koma mace, to dole a barshi ya shiga ban dakin da yayi daidai da halittar da aka canza masa.

Su kuma jihar ta Carolina ta Arewa sai ta fito da dokarta mai cewa, idan tun farko takardar shaidar haihuwar mutum ta nuna cewa, shi namiji ne ko mace, to dole ko yasa an maida shi sabanin jinsin, sai dai ya shiga ban dakin jinsin da takardar haihuwarsa ta nuna.

A jiya Litinin, babbar Atoni-Janar ta Amurka Loretta Lynch ta kira dokar tsangwamar da jihar ta dau nauyi da cewa, ta tuna mata lokacin da ake tsangwamar bakaken fatar Amurka na haramta musu shiga wuraren walwalar jama’a, ko kuma hukuma ce zata fadi mutumin da zaka iya aura.

Gwamantin tarayyar ta maka sunayen wadanda take kara, kama daga Gwamnar jihar Pat McCrory da Ma’aikatar Kare Lafiyar Jama’a da kuma Jami’ar Carolina ta Arewa, wacce ta karbi tallafin Miliyoyin kudi daga gwamnatin tarayya.

Suma jihar sun shigar da karar gwamnatin tarayya a jiya Litinin don kare dokar tasu ta jihar, sannan suka kara da cewa gwamnati tarayya tana yiwa mutane barazanar bayyanin daidaiton jinsi, bayan ba wata hujjar da ta nuna daidaiton jinsin.

XS
SM
MD
LG