Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Sudan Ta Kudu Ta Ayyana Shirin Tsagaita.


Shugaba Silva Kiir na sudan ta kudu da takwarorinsa na Kenya da Ethiopia
Shugaba Silva Kiir na sudan ta kudu da takwarorinsa na Kenya da Ethiopia
Kungiyar hada kai da ci gaban kasashen Afirka na yanki, tace gwamnatin Sudan ta kudu ta amince da shirin tsagaita wuta, mataki da ake gani zai iya taimakawa wajen kawo karshen fadar kabilanci wanda ya halaka fiye da mutane dubu daya cikin watan nan.

Kungiyar nan mai lakabin IGAD ce ta bada snarwar haka bayan ta kammala wani taron koli da ta kira a birnin Nairobi jiya jumma’a. Kungiyar tayi kira ga magoya bayan shugaba Silva Kirr, da mgoaya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar, suma su ayyana wannan mataki.

Machar bai halarci taron ba, kuma bai bada wata sanarwa nan da nan ta maida martani kan wannan kira da taron kolin yayi ba.

Ahalinda ake ciki kuma ayarin farko na karin sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD sun isa Sudan ta kudu a jiya jumma’a. MDD tace karin jami’an tsaro 72 ‘Yansanda daga kasar Bangladesh sun isa kasar daga jamhuriyar demokuradiyyar kwango. A makon jiya ne kwamitin sulhu na MDD ya amince da kara sojojinta a Sudan ta kudu na wucin gadi zuwa dubu 14, daga dubu takwas ahalin yanzu.

A wani lamari na daban a Sudan ta kudu din wani dan jarida a Sudan ta kudu ya bayyana irin mummunar tarzomar da tilas ta masa da iyalinsa gudu zuwa cikin daji.
Da yake magana d a sashen turanci na MA mai yada shirye shiryensa zuwa ga nahiyar Afirka, David Mayar ya fada jiya jumma’a cewa sojoji sun harbe shi ranar Alhamis yayinda shi da iyalinsa suke kokarin komawa garinsu Bor.

Mayar yace bisa kuskure sojojin gwamnati wadanda suke da alamun maye suka harbe shi.

Mayer ya sami jinya daga raunind a ya samu a wani sansanin MDD dake garin na Bor.
Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG