Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Turkiyya Ta Tsare Editan Jaridar Cumhuriyat


Shugaban kasar Turkiyya
Shugaban kasar Turkiyya

Yau Juma’a gwamnatin kasar Turkiyya ta tsare babban jami’in gudanarwar jaridar Cumhuriyat, bayan da ta tsare wasu ma’aikatan ta su 9 a cikin makon da ya gabata, kamar yadda jaridar ke cewa.

‘Yan sanda sun kame babban jami’in Akin Atlay a babbar tashar jirgin saman Istanbul, jim kadan da saukar sa daga jirgi lokacin da yake dawowa daga Jamus.

Suna cewa jaridar Cumhuriyar ita ce sahun gaba wajen sukar lamirin jamiyyar AKP ta shugaba Racep Tayip Erdowan.

Jaridar tace bayan an dan tsare shi Atlay na dan wani lokaci a tashar jirgin, daga bisani kuma aka umurce shi da ya shiga motar ’yan sanda wadda ta kai shi ofishin su dake birnin Istanbul, tace ance an tsare dashi ne domin tuhumar cewa jaridar tana da alaka da ayyukan ‘yan ta’adda.

Yanzu haka dai manya-manyan jami’an jaridar su tara suna tsare ciki har da babban Editan ta Murat Subuncu har sai abin da bincike ya nuna.

Tsare wadannan mutanen dai ya haifar da cece kuce a sassan duniya dabanm-daban akan take hakkin bil adama a kasar dake da nasaba da fadin albarkacin baki.

XS
SM
MD
LG