Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hafsan hafsoshin sojojin Faransa ya gana da shugaban Kamaru


Paul Biya, shugaban Kamaru
Paul Biya, shugaban Kamaru

Hafsan hafsoshin kasar Faransa Janar Pierre de Vila ya kai ziyara kasar Kamaru inda ya gana da shugaban kasar Paul Biya

Hafsan hafsoshin kasar Faransa Janar Pierre de Vila ya kai ziyara kasar Kamaru akan fitinar Boko Haram.

Shi dai janar Pierre de Vila tare da jakadan kasar Faransa dake Kamaru sun kaiwa shugaban Kamaru din Paul Biya ziyara a fadarsa dake babban birnin kasar wato, Yaounde.

Janar de Vila ya yi ganawar siri da shugaban Kamaru din. Sun kwashe fiye da sa'o'i hudu suna tattaunawa. Muhawarar tasu ta karkata ne akan duk abubuwan da za'a yi a kakkabe 'yan ta'adan Boko Haram da suka addabi kasar. Ita dai kungiyar Boko Haram da ta samo asali daga Najeriya ta tada rigingimu a Najeriya da Kamaru da Nijar da ma Chadi.

Kasashen Nijar da Kamaru zasu kara kaimin dankon zumunci domin fuskantar kungiyar Boko Haram. Zasu hada karfi da karfe a bangaren diflomasiya da tsaro.

A wannan sabuwar shekara dai kasar Faransa ta dauki matakin farko na ganawa da kasar Kamaru.

Daga karshe shugaban Kamaru Paul Biya ya makalawa Janar de Vila lambar yabo da zummar cewa shi ma dan kasa ne nagari.

Da yake jawabi Janar de Vila yace ya kawo ziyarar ce domin tattaunawa da jami'an tsaro akan yadda zasu kawar da 'yan ta'ada da aikin ta'addanci a yankin musamman 'yan kungiyar Boko Haram da makamantansu. Yace babu tsaro idan babu cigaba kuma babu cigaba idan babu tsaro.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG