Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hajiya Maryam Sani Abacha Ta Yaba Sakin Al-Mustapha


Maj. Hamza Al-Mustapha leaves the court after a verdict in Lagos, Nigeria, on Monday, Jan. 30, 2012.
Maj. Hamza Al-Mustapha leaves the court after a verdict in Lagos, Nigeria, on Monday, Jan. 30, 2012.

Uwargidan tsohon shugaban kasar Najeriya Sani Abacha ta yaba sakin Hamza Al-Mustapha

Uwargidan tsohon shugaban kasar Najeriya Maryam Sani Abacha ta bayyana farin cikin sakin Majo Hamza Al-Mustapha babban dogarin janar Sani Abacha, bayan ya shafe shekaru 14 a gidan yari.

Sakin Al-Mustapha ya biyo bayan soke hukumcin kisa da kotun daukaka kara tayi jiya karkashin jagorancin mai shari’a Rita Pamu wadda ta wanke Mojo Hamza Al-Mustapha da kuma Lateef Shofolahan da ake tuhuma da kisan Kudirat Abiola, matar hamshakin tsohon dan kasuwar kuma da ya tsaya takarar shugaban kasa Mohood Abiola.

A cikin hirarsu da wakilinmu Saleh Shehu Ashaka jim kadan bayan sanar da sakinsu Hajiya Maryam Sani Abacha ta kuma yi addu’a Allah ya tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:12 0:00
Shiga Kai Tsaye
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG