Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Babu Labarin Daliban Cibok


Daya daga cikin iyayen Cibok tana zubar da hawaye a gaban Majalisar Kasa, a birnin Abuja dake Najeriya.
Daya daga cikin iyayen Cibok tana zubar da hawaye a gaban Majalisar Kasa, a birnin Abuja dake Najeriya.

Hukumomin arewacin Najeriya sun ce har yanzu babu labarin 'yan mata 'yan makaranta dari biyu da saba'in da shida daga cikin wadanda aka sace a wata makaranta a watan jiya.

Da yamnmacin jiya Alhamis jami'an 'yan sanda da na leken asirin jahar Borno su ka ce yawan 'yan matan da aka sace ya karu, bayan da iyayen yara suka yi korafin cewa adadin da aka bayar da farko yayi kadan.

Kwamishinan 'yan sanda Tanko Lawan ya ce da wuya a iya cewa a zahiri ga adadin 'yan matan da aka sace saboda daliban wasu makarantu ma su na wurin a wannan rana domin yin jarrabawar karshen shekara. Lawan ya ce daga cikin 'yan matan da aka sace hamsin da uku ne suka kubuce suka gudu.

Wani jami'in tsaron kasa mai suna Ahmed Abdullahi, ya ce watakila yawan 'yan matan da aka sace zi ci gaba da karuwa saboda iyaye na ta zuwa daga wasu kauyuka su na bayar da rahoton cewa ba su ga 'ya'yan su ba. Ya ce ba yawan su ne abun damuwa ba, ya ce ko da yarinya daya aka sace dole ne a mayar da hankali a kan ta.

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG