Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-haren da aka kai kan ofisoshin 'yan sanda sun yi sanadin mutuwar mutane biyu


Imam Abubakar Shekau, shugaban 'yan Boko Haram
Imam Abubakar Shekau, shugaban 'yan Boko Haram

‘Yan sanda a arewacin Nijeriya sun ce wasu ‘yan bindiga

‘Yan sanda a arewacin Nijeriya sun ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wasu ofisoshin ‘yan sanda biyu a Kano, har wasu fararen kaya biyu sun mutu.

Hukumomi sun ce an hallaka fararen kayan ne da yammacin jiya Lahadi a yayi harbe-harbe tsakanin ‘yan bindigan da ‘yan sanda. Maharan sun kuma jefa bama-bamai kan ofishin ‘yan sandan, wadanda su ka lalata ofishin.

‘Yan bindigar sun kaddamar da hari na biyu da safiyar yau Litini kan wani ofis din da aka yi fakonsa a makon jiya, to amman babu rahoton jin rauni.

Babu wata kungiyar da ta dau alhakin kai hare-haren nan da nan.

Kungiya mai tsattsauran ra’ayin Islamar nan ta Boko Haram ta ce ita ke da alhakin kai hare-haren ‘yan makwannin da su ka gabata a birni na biyu a girma a Nijeriya wato Kano, inda mutane 185 su ka rasu.

Kungiyar ta Boko Haram ta ce ta na yaki ne don ta kafa tsattsauran tsarin Shari’ar Musulunci a fadin Nijeriya.

Tashin hankalin da ke cigaba da aukuwa ya kawo fargabar cewa Nijeriya, wadda ita ce kasar Afirka da ta fi yawan jama’a da kuma arzikin man fetur, na dosar yakin basasa.

A halin da ake ciki kuma ‘yan kabilar Igbo da ke Nijeriya na wani gagarimin aikin kwasar matansu da yaransu daga arewacin Nijeriya saboda tashin hankalin da ake danganta shi da kungiyar da ke da tsattsauran ra’ayin Islama ta Boko Haram.

Wakilin Muryar Amurka a Yammacin Afirka, Jane Labou, ya bayar da rahoton cewa wannan kwasar mata da yaran ta biyo bayan tarurrukan da shugabannin Igbo su ka yi a karshen mako a Enugu, a inda su ka shawarci magidanta su kwashi mata da yara zuwa gida sannan su tsaya a arewa su kare dukiyoyinsu.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG