Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Sama Ya Barnata Asibitocin Syria Guda Biyar Da Kashe Jariri


Dan Syria Da Gawar Dansa Da Ya Ciro Daga Bangorin Rusassun Ginin Da Harin Sama Na Gwamnatin Syria, Aleppo, July 24, 2016.
Dan Syria Da Gawar Dansa Da Ya Ciro Daga Bangorin Rusassun Ginin Da Harin Sama Na Gwamnatin Syria, Aleppo, July 24, 2016.

Wani hari ta sama na gwamnatin Syria akan yankunan da ‘yan tawaye ke rike da su ya ragargaza wasu asibitoci guda biyar har ya kashe wani jariri tare da saka rayuwar fararen hula sama da dubu 20 a cikin hatsari a yankunan.

Kamar yadda wata kungiyar rajin kare hakkin dan Adam mai suna Observatory for Human Rights ta bayyana.

Tace asibitoci hudu daga cikin biyar din suna yankin birnin Aleppo ne, da kuma wani guda daya a Atareb da ke yammacin babban birnin.

Dakarun gwamnatin Syria hade da sojojin taron dangi sun yiwa birnin Aleppo kawanya tun makon da ya gabata, garin da shekaru hudu kenan ana jani in jaka tsakanin sojojin gwamnati dana ‘yan tawayen kasar.

Wannan lamarin ya haifar da karancin abinci ga fararen hula mazauna wuraren da ke makale a hannun ‘yan tawaye.

Ga kuma rahoton ma’aikatar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace Syria itace ta fi kowace kasa zamewa ma’aikatan lafiya hatsarin shiga don kai dauki.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG