Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hillary Clinton Ta Kara Kaimin Yakin Neman Zabe


Hillary Clinton
Hillary Clinton

Hillary Clinton, ‘yar takaran shugaban kasa ta jam’iyyar Democrats a zaben wannan shekara a Amurka, wadda ke ta samun karfin gwiwar cewa zata lashe zaben, ta fara kutsawa cikin wasu jihohin da, a bisa al’ada, kullum jam’iyyar adawa ta Republican ke lashe su a zabe, da fatar cewa zata kwace su daga hannun abokin takaranta Donald Trump, abin da zai baiwa jam’iyyarta ta damar kwace har da majalisun dokokin kasar ma.

Yanzu ana sauran makkoni ukku a yi wannan zaben, kwamitin kyamfe na Hilary Clinton din ya bada sanarwar cewa zai kashe Dala milyan 2 a cikin jihar Arizona, jihar da sau daya kawai ta taba zabar ‘yan Democrat a cikin zabukka 16 da suka gabata a baya!

Haka kuma Ms. Clinton na shirin aikawa wasu giggan magoya bayanta da suka hada da Michelle Obama, matar shugaban kasar na yanzu, zuwa jihar ta Arizona don suyi mata yakin neman zabe.

Ra’ayoyin jama’a da aka dauka a baya-bayan nan na nuna cewa Clinton da Trump suna kut-da-kut da juna a cikin wannan jihar dake kusa da inda Amurka tayi kan iyaka da kasar Mexico.

Ko bayan Arizona, Clinton na kara kaimi a kyamfen dinta a wasu jihohi biyu na tsakiyar Amurka, inda yanzu haka Trump yake gabanta – watau jihohin Missouri da Indiana.

Kusan dukkan ra’ayoyin jama’a da ake dauka kwanan nan dai suna nuna cewa Hilary Clinton na dab da zama shugabar Amurka, mace, ta farko a tarihin kasar.

XS
SM
MD
LG