Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hosni Mubarak Yace Ba zai Sake Takara Ba


A wan nan hoto daga tashar talabijin ya Masar a muhimmin jawabi da yayi wa al'umar kasar ranar Talata.
A wan nan hoto daga tashar talabijin ya Masar a muhimmin jawabi da yayi wa al'umar kasar ranar Talata.

Shugaban Masar Hosni Mubarak ya bada sanarwar wan nan ne wa’adinsa na karshe a mulkin Masar na shekaru 30.Ajawabi da ya yi yace ba zai sake takarar neman wani sabon wa’adi ba.

Shugaban Masar Hosni Mubarak ya bada sanarwar wan nan ne wa’adinsa na karshe a mulkin Masar na shekaru 30.Ajawabi da ya yi yace ba zai sake takarar neman wani sabon wa’adi ba.

A yammacin jiya Talata ce Mr.Mubarak ya gayawa al’umar kasar ta talabijin cewa ya sadaukadda rayuwarsa kaf yana bauatawa Masar da al’umarta.Bai nuna alamun yana shirin mu murabus ko barin kasar ba.Maimakon haka yace zai yi aiki cikin sauran lokacin wa’adinsa naganin ya mika mulki cikin lumana.

Sanarwar da shugaban ya yi ya kara fusatar da dubun dubatan al’umar kasar da tuni suka cika tituna duk fadin kasar suna nemada ya yi murabus batareda bata lokaci ba.

A alkahira mutane da aka yi kiyasin akalla sun kai dubu metan da hamsin a dandalin Tahiri inda nan ne cibiyar zanga zanga zangar cikin lumana suka fara ihu “katafi Katafi”.Da dama daga cikinsu suka cire takalma suna rike da shi alamar reni a kasar larabawa.

Da zarar kammala jawabinsa ne fada ya barke tsakanin magoya bayan gwanati da msu zanga zanga a birin Alexandria dake arewacin kasae.An jikkata akalla mutane 12.Shaidu suka ce an gwabza irin haka a Suez,da wasu birane a gabshin Alkahira.

Dangwagwarmayar Demokuradiyya Mohammed ElBaradei ya gayawa tashar talabijin ta CNN cewa shawarar da Mr. Mubarak ya yanke na ci gaba da mulki zai tsawaita “damuwa” da Masar take ciki. Har a kai ga zaben shugaban kasa cikin watan Nuwamba.Ya kira matakin rufa rufar mutumoinda bashi da niyyar sauka daga mulki. Ahalin yanzu kuma shugaban Amurka barack Obama yace ya gayawa takwaran aikinsana Masar dake tsaka mai wuya cewa tilas shirin mika mulki cikin tsanaki da lumana a fara shi yanzu.

XS
SM
MD
LG