Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Binciken Sararin Samaniya Ta Amurka NASA Zata Bakunci Duniyar Mars


NASA Administrator Charles Bolden congratulates SpaceX after the rocket was launched successfully. (Reuters)
NASA Administrator Charles Bolden congratulates SpaceX after the rocket was launched successfully. (Reuters)
Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka tana shirin tura wata na’aura zuwa duniyar Mars da asubahin litinin din nan.

Na’urar mai nauyin ton daya, da ake kira Curiosity zata binciki duniyar domin sanin ko akwai halittu, kuma zata tattara wasu muhimman masu muhimmanci. Amma da farko ana fatan zai sauka lafiya bayan wata takwas yana wan nan balaguro.

Masana kimiyya wadanda suke aiki da hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka da ake kira NASA, sun ce saukar na’urar da take gudun kilomita dubu ashiri da daya da dari biyu da arba’in cikin ko wani sa’a daya, shine kalubale fiyeda ko wanne da suka taba fuskanta.
XS
SM
MD
LG