Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kasuwanci (WTO) Ta Duniya Ta Cimma Daidaituwa Kan Kasuwanci A Karo Na Farko


Daraktan WTO Roberto Azevedo yana murnar yarjejeiyar da suka cimma
Daraktan WTO Roberto Azevedo yana murnar yarjejeiyar da suka cimma

A karon farko tun da aka kafata Hukumar Kasuwanci WTO ta cimma daidaituwa kan gudanar da kasuwanci a duniya.

Wakilan kasashen da suka halarci taron Hukumar Kasuwanci Ta Duniya ko WTO, a takaice, da aka yi a Bali kasar Indonesia, sun jimma yarjejeniya dangane da kasuwanci tsakanin kasashen kungiyar yadda kowace kasa zata anfana. Wannan yarjejeniya ita ce irinta ta farko tun da aka kafa hukumar a shekarar 1995.

Daraktan WTO Roberto Azevedo ya yi kwalla yayin bikin rufe taron. Ya ce a karon farko WTO ta yi abun da ya dace, wato ta haifi da mai ido.

Abu mafi mahimmanci da yarjejeniyar ta kunsa shi ne kawo sassauci dangane da ayyukan kwastan na kowace kasa yadda zasu zama da adalci kuma a saukake ba tare da wata tangarda ba. To amma kafin dokar ta soma aiki sai gwamnatocin kasashe 159 dake cikin WTO sun amince.

Taron ya fuskanci barazana daga kasar Cuba wadda ta ce ba zata amince da yarjejeniyar ba idan bata hada da cire mata takunkumin karya tattalin arziki da Amurka ta kakaba mata ba. Sai dai daga baya Cuban ta janye barazanarta.

Masu nazari kan tattalin arziki sun kiyasta cewa yarjejeniyar zata habbaka tattalin arzikin duniya da Dalar Amurka miliyan dubu daya ko tiriliyan daya a kowace shekara.
XS
SM
MD
LG