Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram: Yunkurin Samar Da Hukumar Raya Arewa Maso Gabashin Najeriya


Sansanin 'yan gudun hijira a Dambua.
Sansanin 'yan gudun hijira a Dambua.

Shugabannin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya na kara ba da tabbacin cewa hukumar da aka amince a kafa ta raya arewa maso gabashin Najeriya da rikicin Boko Haram daidaita za ta fara aiki.

Tsarin hukumar da ya samu karbuwa a Majalisar Dattawa shi ne kula da raya tattalin arzikin arewa maso gabas, bayan da Boko Haram ta yi ma yankin illa.

Sakataren jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, ya ce yin wannan hukuma ya kara musu kwarin gwiwar kasancewar ana kan hanyar cika alkwaruwan da aka dauka lokacin yakin neman zabe.

Dan yankin arewa maso gabas Mohammadu Inuwa Yahaya, ya yi na’am da matsayin inda ya ce sun ganewa idanunsu irin matsalolin da yankin ya shiga, wasu sun rasa gidajensu da iyalensu, wanda yanzu haka wasu mutanen suna zaune cikin kunci a sansanonin ‘yan gudun hijira.

A cewar CSP Ado Ibrahim Gabanni mai ritaya, hukumar za ta yi nasara ne kawai idan har ta taimakawa matasa su daina bara ko gararanba akan tituna.

Ana sa ran hukumar za ta yi aiki kamar takwararta dake kula da yankin Niger-Delta, NDDC.

Haka kuma wata hukumar da ta kasa kai labari ita ce ta kula da jihohi masu samar da lantarki.

Ga rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG