Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Nijar Sun Yabi Matasa Game Da Ta'addanci


Tambarin Jamhuriyar Nijar
Tambarin Jamhuriyar Nijar

Matasan Maradi sun yi alkawarin cewa ba za'a yi amfani da su a yi ta'addanci ba, a cewar Mahaman Siraji Moussa daga Maradi, a dai-dai wannan lokaci da Janhuriyar Nijar take daura dammarar yaki da 'yan ta'addan Boko Haram.

Ganin yadda 'yan kungiyar Boko Haram suka bayyana a yankin Diffa, kasar jamahuriyar Nijer, suka tursasawa dubban mutane gudu daga gidajen su, yanzu haka hukumomin Maradi, sun fara fadakar da matasa su guji shiga kungiyar ta'addanci.
Mataimakin shugaban Majalisar dokokin yankin Maradi, Mahaman Siraji Moussa ya shaidawa wakilin Sashen Hausa Chaibou Mani cewa matasa sun yi tururuwa sun amsa kira tare da yin alkawarin cewa ba za su yarda a yi amfanin da su a yi ta'addanci ba.
Duka wannan na faruwa ne adaidai lokacin da gwamnatin kasar Nijer ta dauki tsaurara matakan tsaro a yankin Diffa inda sojoji ke artabu da 'yan Boko Haram.
Mallam Mahaman Siraji Moussa ya kara jaddada mahimmancin addu'a tare da yin kira ga jama'a da su tashi haikan su dage da rokon Allah, Ya kare Maradi daga sharrin ta'addanci, Ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk kasar jamahuriyar Nijer, da ma duniya baki daya:
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG