Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Sun Zartas Da Hukuncin Kisa Akan 'Yan Bindiga A Somaliya


Sojojin Somaliya
Sojojin Somaliya

Hukumomin lardin Puntland sun aiwatarda hukuncin kisa akan wasu ‘yan kishin Islama su 13 da aka same su da laifin kisan kai.

Wadanan mutanen 13 da suka hada maza 12 da macce daya, an bindige su ne har Lahira a cikin asiri da misalin karfe 3 na dare a wajen garin Bosaso.

Kwamishionan Hukumar kotunan yiwa ‘yan kishin Islama shara’oi na yankin, Abdi Fatah Haji Adam ya gaya wa sashen Somaliyanci na nan VOA cewa an sami wadanan mutanen ne da laifin kisan mutane da dama da suka hada da wani shahin malami da wasu ‘yanmajalisar dokoki da kuma jami’an tsaro.

Duk da cewa sojojin hadin gwaiwa na ita Somalia din da Ethiopia da na sauran kasashen Afrika tuni suka darkaki mayakan al-Shebab suka fice daga aksarin manyan birane da alkaryun Somalia, haer yanzu ‘yan wannan kungiyar dake da daurin gindin al-Qaida suna ci gaba da gudanarda aiyukkansu a wurare da dama.

Ko makkoni biyu da suka wuce ma al-Shebab ta fito fili tana bugun gaban cewa itace ta kashe wasu mutane kamar 30 a lokacinda ta kai farmaki a Mogadishu, babban birnin kasar.
XS
SM
MD
LG