Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Najeriya Sun ce Tattalin Arzikin Kasar Ya Habaka


Ngozi Okonjo-Iweala, ministar harkokin kudin Najeriya.
Ngozi Okonjo-Iweala, ministar harkokin kudin Najeriya.

A wani sabon kidid-diga, Najeriya tace tattalin arzikinta ya hakaba har ma yafi na kasar Afirka Ta Kudu.

Hukumomin Najeriya sunce kasar ta wuce Afirka ta kudu a zaman kasar da tattalin arzikinta ya dara na ko wace kasa a nahiyar Afirka.

Babban masanin alkaluma a Najeriya, Yemi Kale, ya fada ran Lahadi cewa ana kiyasin tattalin arzikin Najeriya ya kai kusan dala miliyan dubu 490, wanda ya zarta Afirka ta kudu, kasar da Bankin duniya yayi kiyasin tattalin arzikinta, ya kai dala miliyan dubu 384 a shekara ta 2012.

Kamar yadda zaku ji cikin wannan rahoto da Nasiru Adamu El-Hikya ya aiko mana.
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG