Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ibrahim Babangida Da Olusegun Obasanjo Sun Gana Kan Tsaro A Najeriya


Tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida
Tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Tsoffin shugabannin biyu sun zauna suka yi shawara kan hanyoyin da suka fi dacewa na kawo karshen tashe-tashen hankula da zub da jini a kasar

Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, sun gana na tsawon lokaci domin tattauna matsalolin tsaro da suka dabaibaye Najeriya a daidai wannan lokacin.

Da yake tabbatar da wannan ganawa ta su ga masu neman labarai, Janar Babangida ya ce ya kamata kowane dan Najeriya ya sanya hannu a kokarin kawo karshen wannan ukuba da ta far ma kasar.

A wata hirar da yayi da wakilin Muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari, janar Babangida ya ce zasu ci gaba da wannan kokari nasu, kuma ko da ta kama ne ma, zasu sake sanya rigunansu na soja domin tabbatar da ci gaba da dorewar Najeriya a zaman kasa daya.

Ga bayanin Janar Babangida a wannan hira ta su...

Batun Tsaro A Najeriya

Hira Da Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG