Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ICC ta yi watsi da tuhumar da ake yiwa mataimakin shugaban kasar Kenya


William Ruto mataimakin shugaban kasar Kenya da kotun kasa da kasa ta yi watsi da tuhumar da ake yi masa
William Ruto mataimakin shugaban kasar Kenya da kotun kasa da kasa ta yi watsi da tuhumar da ake yi masa

Kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa ko ICC tayi watsi da tuhume tuhume da ake yiwa mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto da ake zargi da laifin gallazawa bil’adama.

Jiya Talata kotun ICC tace alkalai buyu daga cikin uku sun kada kuri’ar amincewa da yin watsi da karar da aka kai Ruto da wanda ake tuhumarsu tare Joshua Arap Sang.

An dorawa Ruto alhakin kisan kai da tilastawa al’umma kaura da kuma gasawa jama’a akuba yayin tashin hankali a shekara ta dubu biyu da bakwai da dubu biyu da takwas da suka biyo bayan zabe a Kenya.

An kuma zargi Sang, shugaban wata tashar gidan radio da aikata wannan laifin.

An kashe kimanin ‘yan kasar Kenya dubu daya da dari daya a rikicin kabilanci na tsawon mako guda da ya biyo bayan zaben.

An zargi shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta da taka rawa a kitsa tashin hankalin, aka kuma tuhumeshi da laifuka biyar na gallazawa bil’adama. A watan Maris shekara ta dubu biyu da goma sha biyar kotun shari’anta manyan laifuka ta kasa da kasa ta yi fatali da karar bayanda masu shigar da kara a kotun suka janye karar sabili da rashin kwararan shaidu.

Masu rajin kare hakkin bil’adama suna zargin gwamnatin kasar Kenya da rashin ba masu shigar da kara hadin kai da kuma tsorata shaidu.

XS
SM
MD
LG