Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ICC Tayi Hukunci Akan Germain Katanga


​Kotun kasa da kasa, ICC ta yankewa tsohon shugaban yan yakin sa kai na kasar Congo Germain Katanga hukuncin dauri shekaru goma sha biyu a gidan yari, a saboda rawar daya taka a kisan kiyashin da aka yi a shekara ta dubu biyu da uku.

A watan Maris aka samu Katanga da laifin taimakawa wajen tsara yan yakin sa kan, da suka kashe kimamin mutane dari biyu a kauyen Bogoro dake gabashin jamhuriyar Kwango.

Kotun tace Katanga ya aikata laifufukan yaki da musgunawa bani Adamu, ciki harda yin kisa da kai hare hare akan farar hula da lalata dukiyoyin jama'a.

Tuni dama shi Katanga yayi shekaru bakwai a daure. A saboda haka, alkali Bruno Cote ya yanke hukunci a yau juma'a cewa za'a debe shekaru da ya riga yayi daga hukuncin da aka yanke masa.

Shi dai Katanga, dan shekara talatin da shidda bai amsa cewa ya aikata wadannan laifuffuka ba, yana mai fadin cewa shi bashi da iko akan mayakan. Tuni lauyoyinsa suka daukaka karar hukuncin da aka yanke masa.

Katanga wanda yake da lakabin "Simba", shine mutum na biyu da kotun kasa da kasa ICC ta yankewa hukunci tun lokacinda ta fara shariar laifuffukan yaki a shekara ta dubu biyu da biyu.
XS
SM
MD
LG