Accessibility links

Akan karin lokacin Madina Dauda ta tattauna da Mr. Nick Dazan, jami'in yada labaran hukumar INEC.

K'arshen ta dai hukumar zaben Najeriya mai zaman kan ta, INEC a takaice, ita da kan ta, ta ga cewa akwai bukatar daukan matakin tsawaita lokacin raba katunan zaben dindindin, hakan kuwa a daidai lokacin da d'imbin 'yan Najeriya ke ta kuka da korafin cewa ba su samu katunan su ba har yanzu ana sauran 'yan kwanaki k'alilan a yi zabe.

Madina Dauda ta tuntubi jami'in yada labaran hukumar zaben Najeriya, INEC, wato Mr. Nick Dazan, ta yi mi shi tambayoyi masu yawa kuma masu ma'ana game da wannan hali da ake ciki, na ga zabe na zuwa, kuma miliyoyin mutane ba su samu katunan su ba.

Mr. Nick Dazan ya ce duk wanda ya samu jami'an su ba sa yin aikin da aka sa su kamar yadda ya kamata , a shaida musu, za su gaggauta daukan mataki a kan su.

XS
SM
MD
LG