Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran ta baiwa hukumar makamashi takardun bayanai.


Mashawarcin nukuliyan Iran, Abbas Araghchi
Mashawarcin nukuliyan Iran, Abbas Araghchi

Iran ta baiwa hukumar makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya da ake cewa IAEA a takaice takardun da aka danganta da zarge zargen da ake yi mata cewa tayi ko kuma tana kokarin kera makaman atom.

Kasar Iran ta baiwa hukumar makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya da ake cewa IAEA a takaice takardun da aka danganta da zarge zargen da ake yi mata cewa tayi ko kuma tana kokarin kera makaman atom.

Matakin daya sa ta cimma wa'adin gamsar da ka'idodin da aka gitta mata na sausauta takunkunmin da aka aza mata kamar yadda yarjejeniyar data kula da giggan kasashen duniya a watan jiya ta tanada.


Jiya Asabar Iran ta mikawa hukumar IAEA bayanai a rubuce da kuma takardu kamar yadda aka cimma yarjejeniya a tsawirar baiyana aiyukanta data yi a baya da kuma yanzu da suka shafi shirin nukiliyar kasar. Hukumar IAEA ta tabbatar a jiyar Asabar cewa Iran ta cimma wa'adin mika bayanan.


Bayanai da Iran ta gabatar sun hada harda bayanai cewa da kyar ne ta karyar alkawarin data yi kamar yadda ta sha yi a baya.


Taswirar ta kuma tanadin cewa akwai yiwuwar hukumar makamashin ta nemi karin bayani daga iran kan ranar sha biyar ga watan oktoba domin hukumar ta rubuta rahotanta na karshe kan karshen wannan shekara idan Allah ya kaimu.

XS
SM
MD
LG