Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iraniyawa Sun Yiwa Shugaba Rouhani Kyakkyawar Tarba


Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani

Daruruwan Iraniyawa suka yi tururuwa domin tarbar shugaban kasar Hassan Rouhani bayan tattaunawarsu ta tarihi da shugaban Amurka Barack Obama.

Daruruwan Iraniyawa suka yi tururuwa domin tarbar shugaban kasar Hassan Rouhani bayan tattaunawar da suka yi ta tarihi da shugaban Amurka Barack Obama.

Sai dai rahotanni daga kafafen sadarwar na kasar Iran na nuni da cewa, wadansu masu tsats-tsauran ra’ayi kalilan sun yiwa Amurka allah wadarai, wadansu kuma suka rika jifar ayarin shugaban kasar har da takalma lokacin da yake barin tashar jirgin sama ta Tehran yau asabar.

Mr. Rouhani ya koma gida ne bayan halartar taron shekara shekara na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.
Kafin ya bar New York, jiya jumma’a, Mr. Rouhani da Mr. Obama suka yi magana ta wayar tarho na tsawon mintoci goma sha biya. Wannan ce tattaunawa ta farko kai tsaye da shugabannin Iran da na Amurka suka yi cikin kusan shekaru talatin da biyar, abinda wadansu suke gani a matsayin wata ci gaba ta warware takaddamar diplomasiya tsakanin kasashen biyu.

An daina duk wata huldar diplomasiya tsakanin amurka da Iran ne bayan juyin juya halin daular Islaman a shekara ta dubu da dari tara da saba’in da tara da ya kawo karshen masarautar da kuma matakin da masu zanga zanga suka dauka na mamaye ofishin jakadancin Amurka da yin garkuwa da Amurka na tsawon sama da shekara daya.

Dandanlin sadarwar twitter na Mr .Rouhani ne ya sanar da tattaunawar ta tarihi.

Mr. Obama yace shugabannin kasashen biyu sun tattauna a kan yunkurin cimma matsaya a kan shirin nukiliya na kasar Iran.
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG