Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isira'ila Ta Kai Hari A Siriya


Wani jirgin yakin Isira'ila
Wani jirgin yakin Isira'ila

Jami’ai a Isira’ila sun ce Isira’ilar ta kai hari kan wasu kayan yakin da Syria ta yi niyyar kai ma ‘yan Hezbollah

Jami’ai a Isira’ila sun ce Isira’ilar ta kai hari kan wasu kayan yakin da Syria ta yi niyyar kai ma ‘yan Hezbollah, kungiyar mayaka da ke kasar Lebanon.

Jami’an na Isira’ila sun yi maganar ce a sakaye, amma gwamnatin Isira’ila ba ta fito a hukumance ta amsa cewa ta kai harin ba. Jami’ai a yankin sun ce ba makaman guba aka auna a harin ba.

Jami’an Amurka sun gaya wa kafofin yada labaran yammacin duniya cewa babu alamar saida jiragen saman Isira’ila su ka shiga sararin saman Syria kafin su ka kaddamr da harin. Su ka ce harin ya auku ne da yammacin Alhamis ko kuma safiyar Jumma’a.

Jami’an Amurka sun ce da alamar an auna wani wurin tara makamai ne. Jami’an Syria dai sun gaya ma kafafen yada labarai cewa bas u da wata masaniya game da harin.

Hezbolla na da alaka da gwamnatin Shugaban Syria Bashar al-Assad. Kungiyar mayakan, wadda ke samun goyon bayan Iran, ta fafata wani takaitaccen yaki da Isira’ila a 2006.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG