Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ISIS Na Kara Cafke Wasu Sassan Iraqi


Masu goyon bayan kungiyar ISIS
Masu goyon bayan kungiyar ISIS

Yadda kungiyar ISIS ke cigaba da kwace wasu sassan kasar Iraqi na daurewa jami'an Amurka kai.

Bisa ga dukan alamu, yunkurin shawo kan kungiyar ISIS ya daurewa jami’an Amurka kai, bayanda kungiyar ta sake kwace wani birni a Iraqi.

Jami’an kasar Iraqi sun ce kungiyar ISIS ta kwace wadansu kauyuka uku a garin Ramadi dake lardin Anbar na yammacin kasar jiya Alhamis, yayinda mayakan ke ci gaba da gumurzu da dakaru suna kokarin kwace birnin.

Tuni jami’an IraqI suka bayyana lamarin Ramadi a matsayin wanda ya yi muni, suka ce, a kalla iyalai dubu biyu ne suka kaura domin neman mafaka a Bagadaza babbban birnin kasar. Wadansu sun ce birnin Ramadi ya zama kago.

XS
SM
MD
LG