Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ISIS: Ta Fitar da Wani Faifai wai daga Shugabanta


Abu Bakr al-Baghdadi shugaban kungiyar ISIS
Abu Bakr al-Baghdadi shugaban kungiyar ISIS

Tun watan Nuwamban bara ba'a sake jin duriyar shuagaban ISIS ba sai jiya da ta fitar da wani faifai inda tace sako ne gada shugabanta zuwa ga musulman duniya

Kungiyar ISIS ta saki wani fefe da take ikirarin sako ne daga shugabanta Abu Bakr al-Baghdadi, mutumin da aka juma ba’a ganshi a bainar jama'aba ko aka ji daga gareshi na tsawon watanni.

Sakon ya bukaci musulmi da su tashi suyi yaki a madadin kungiyar kuma suyi hijira zuwa yankin kasashen Syria da Iraqi data kama ta ayyana a zaman "daular Islama".

Yace "musulmai basu da wata hujja na kin daukar makamai na kare kungiyar" a yakin da ta ke yi.

Kafofin yada labarai na yammacin duniya sun gaza tantance ko muriyar ta al-Baghdadi ce.

al-Baghdadi ya bada sako na karshe da muryarsa cikin watan Nuwamban bara, kwanaki bayan da jami'an kasar Iraqi suka ce an jikkatashi a wani farmaki da jiragen yaki da aka kai kan wani gari dake kusa da kan iyakar kasar da Syria.

A ranar Laraba ma'aikatar tsaron Iraqi ta bada labarin cewa wani farmaki da jiragen yakin kasashen da suke taron dangi a yaki da ISIS sun kashe wani mukaddashin kwamandan kungiyar ta ISIS.

XS
SM
MD
LG