Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Kashe Falasdinawa Hudu


Rundunar sojojin Isra’ila ta kashe Falasdinawa hudu sanye da kayan iyo a cikin ruwa dab da gabar Gaza, yayin da Turkiyya ke kokarin kara matsin lamba kan Isra'ila dangane da kashe 'yan rajin kare Falasdinawa 9 da ta yi.

Rundunar sojojin bani Isra’ila ta kashe wasu Falasdinawa hudu ‘yan kishin Falasdinu sanye da kayan iyo a cikin ruwa dab da gabar Gaza. Kungiyar Hamas ta ce an tsinci gawarwaki hudu, yayin da mutum guda ko biyu suka bace.

Rundunar sojojin bani Isra’ila ta ce sojojinta na ruwa sun birkita wani harin da a cewarta wasu ‘yan ta’adda sanye da kayayyakin iyo a ruwa suka yi niyyar kaiwa. Majiyoyin Falasdinawa sun ce mutane hudun da aka kashe ‘yan kungiyar nan ce ta Birged din ‘yan shuhada’u ta al-Aqsa, wadda bangare ce ta kungiyar Fatah ta shugaba Mahmoud Abbas. Kungiyar ta ce mutanen su na atusaye cikin dare ne a lokacin da aka kashe su.

Wannan lamarin yazo mako guda a bayan da sojojin kundumbala na Isra’ila suka kashe ‘yan rajin kare hakkin Falasdinawa su 9 a cikin wanji jirgin ruwan Turkiyya mai suna Mavi Marmara, wani bangare na kwambar jiragen ruwan da suka yi kokarin bijirewa killace Gaza da Isra’ila ta yi domin su kai kayan agaji kai tsaye zuwa yankin.

A halin da ake ciki, ana sa ran Turkiyya zata kara matsin lamba kan Isra’ila dangane da wannan harin a lokacin wani taron kolin tsaro. Turkiyya ta ce zata rage huldar soja da ta cinikayya da Isra’ila idan kasar ba ta nemi gafarar harin na makon jiya ba.

XS
SM
MD
LG