Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Tawagar Shugabannin Kasashe Dake Yammacin Afirka Zasu Bukaci Gbagbo Ya Sauka.

Shugaban Jamhuriyar Benin Boni Yayi da PM Laurent Gbago ya tariyeshi a babbar tashar jiragen sama dake Abidjan,kamin ya gana da Gbagbo da kuma Alassane Ouattara.
Shugaban Jamhuriyar Benin Boni Yayi da PM Laurent Gbago ya tariyeshi a babbar tashar jiragen sama dake Abidjan,kamin ya gana da Gbagbo da kuma Alassane Ouattara.

Yau Talata ce ake sa ran wata tawagar shugabannin kasashe dake yammacin Afirka zasu bukaci shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo ya mika wuya, ya yi na’am da sakamkon zabe dake nuna abokin hamayyarsa ne ya lashe zaben kasar, da aka yi cikin watan jiya.

Talatan nan ne shugabanni daga kasashen Saliyo, Cape Verde,da Benin,suke tattaki zuwa Abidjan. Suna ziyarar ce a madadin kungiyar raya tattalin arzikin kasashe dake yammacin Afirka,watau ECOWAS. Kungiyar tayi barazanar amfani da karfi ta tilastawa Mr. Gbagbo ya sauka kan karagar mulki.

Ana sa ran shugabannin su gabatarwa Mr. Gabgbo tayin bashi mafaka idan ya amince ya yi murabus.

Abokin hamayyar Gbagbo, Alasanne Ouattara, litinin din ce ya yi kira ga ‘yan kasar su fara yajin aiki na gama gari domin tilastawa shugaba Gbagbo ya sauka daga kujerar mulki.

XS
SM
MD
LG