Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gbagbo Yana Zargin Kasashen Duniya Da Yunkurin Kifarda Gwamnatinsa

Sojojin Majalisar Dinkin Duniya a sansaninsu dake birnin Abidjan.
Sojojin Majalisar Dinkin Duniya a sansaninsu dake birnin Abidjan.

Shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo yana zargin shugabannin kasashen Duniya da shirya makarkashiyar hambare shi,bayan gardama da ta biyo zaben kassar.

Shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo yana zargin shugabannin kasashen Duniya da shirya makarkashiyar hambare shi,bayan gardama da ta biyo zaben kassar.

A sakon sabuwar shekara da ya bayar aka karanta ta kafofin yada labaran kasar,shugaba Gbagbo yace bai taba ganin irin wan nan katsa-landan cikin harkiokin cikin gidan wata kasa ba.

Abokin hamayyarsa, mutuminda duka Duniya ta amince shine ya lashe zaben kasar Alassane Ouattara, shima ya fidda nasa sakon na shiga sabuwar shekara,yana cewa abin bakin ciki ne ganin yadda aka kare 2010.

Yace Mr. Gbagbo yaki ya amince ya sha kaye, saboda haka yana ci gaba da kunyata Afirka.

Frayim Ministan gwamnatin Mr. Ouattara, Guillaumo Soro, yace sun baiwa Mr.Gbagbo wa’adin daga yanzu zuwa tsakar daren Jumma’a ya bar mulki ba tareda barazana kan lafiyarsa ba.

XS
SM
MD
LG