Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Baiwa Laurent Gbagbo Mafaka


Shugaban Amurka Barack Obama yake magana ta woya a ofishin shugaban kasa da ake kira Oval Office.
Shugaban Amurka Barack Obama yake magana ta woya a ofishin shugaban kasa da ake kira Oval Office.

Shugabannin Afirka sun tattauna da shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast jiya litinin kamar yadda suka tsara, harma sun yi masa alkawarin yi masa afuwa muddin dai zai amince ya mika ragamar mulki hannun abokin takararsa da yaci zaben shugaban kasa,Alassane Ouattara.

Shugabannin Afirka sun tattauna da shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast jiya litinin kamar yadda suka tsara,harma sun yi masa alkawarin yi masa afuwa muddin dai zai amince ya mika ragamar mulki hannun abokin takararsa da yaci zaben shugaban kasa,Alassane Ouattara.

Wannan shine karo na biyu ke nan da shugabannin kasashen Benin,da Cape Verde,da Saliyo ke kaiwa Laurent Gbagbo ziyara suna tattaunawa dashi,a jiya litinin kuma friministan Kenya Raila Odinga yaje ya riskesu domin shawo akan Mr.Gbagbo. Mai magana da yawun ofishin Odinga yace shugabannin na Afirka sun baiwa Laurent Gbagbo alwashin kare lafiyarsa muddin ya amince ya mika ragamar mulki.

Yayinda ake cikin wnanan halin ne kuma jiya litinin Amurka ta bada sanarwar cewa ashirye take da ta taimakawa Laurent Gbagbo ficewa cikin aminci da karramawa daga kasar Ivory Coast idan har ya yarda ya mika ragamar mulki, Amurka tayi alkawarin bashi mafaka zuwa Amurka,amma Amurka tace lokaci yana neman kurewa Laurent Gbagbo.

XS
SM
MD
LG