Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu Thabo Mbeki Yana Ivory Coast A kokarin Warware Rikicin Siyasar Kasar Da Yake Kara Tsanani.


Sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya daga kasar Jordan suke gadin a kofar waniO'tel aAbidjan
Sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya daga kasar Jordan suke gadin a kofar waniO'tel aAbidjan

Yau Lahadi ce Mr.Mbeki ya isa birnin Abidjan kwana daya bayan da duka 'yan takarar biyu suka ce sun yi rantsuwar kama aiki.

Tsohon shugaban kasar Afirka ta kudu Thabo Mbeki, yana Ivory Coast domin shiga tsakani a kokarin neman hanyoyin warware rikicin siyasare kasar dake kara tsanani.

Yau lahadi ce Mr.Mbeki ya isa birnin Abidjan, kwana daya bayan da dukkan ‘yan takaran biyu a zaben na fidda gwani da aka yi makon jiya, suka bada sanarwar sun yi rantsuwar kama aiki.

An rantsar da shugaba Laurent Gbagbo ne bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben da kashi 51 cikin dari na kuri’u da aka kada. Amma ita kuma hukumar zaben kasar tun farko ta bada sanarwar cewa shugaban ‘yan hamayya Alassane Outtara ne ya sami nasara.

Faransa,Amurka,TT,da kuma Tarayyar Afirka duk sun amince da zaben Mr. Ouattara,suka kuma yi kira ga Mr. Gbagbo ya amince da sakamkon zaben.

Mr. Mbeki wanda Tarayyar Afirka ce ta tura shi domin shiga tsakanin,ana sa ran zai gana Mr. Ouattara da kuma shugaba Gbagbo a yinin yau lahadi.

Sojojin kasar sun kafa shingaye kan titunan birninna Abidjan.Dama tuni birnin yana karskashin dokar hana yawo da dare,kuma an hana dukkan kafofin yada labarai daga ketare aiki.

PM Guillaume Soro,wanda tsohon madugun ‘yan tawaye ne wanda ya yi mulkin daunin iko da Shugaba Laurent Gbagbo, ya bayyana goyon bayansa ga Mr.Ouattara.

Mazauna birnin na Abidjan sun bada labarin jin harbe harbe cikin dare. Jiya Asabar magoya bayan Mr. Ouattara a yini na biyu a jere suka cika tituna suna kona tayoyi,da kuma kafa shingaye.

XS
SM
MD
LG