Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadan Birtaniya a Najeriya Ya Gargadi Masu Neman Juyin Mulki Su Bi Hanyar Dimokradiya


Firayim Ministar Birtaniya Theresa May
Firayim Ministar Birtaniya Theresa May

Cikin 'yan kwanakin nan ne hafsan sojojin Najeriya ya ja kunnuwan wasu sojoji da ya zargi wasu 'yan siyasa da yin zawarcinsu da zummar aikata abun da ba daidai ba kana yace suna gudanar da bincike irin nasu na sojoji

Biyo bayan gargadin na hafsan soji, Jakadan Birtaniya a Najeriya shi ma ya gargadi 'yan Najeriya cewa tsarin dimokradiya a Najeriya wani abu ne mai tsada da za'a yi wasa dashi ba.

Inji Jakadan duk wadanda basu gamsu da salon mulkin wannan gwamnatin ba su bi tsarin dimokradiya wajen kawar da ita ko su jira lokacin zabe amma ba ta hanyar juyin mulki ba da karfin soji.

Kwararre kan sha'anin harkokin kasa da kasa Ambassador Suleman Dahiru ya kalli gargadin ta fuskar diflomasiya.

Yana mai cewa kasashen irin su Birtaniya suna da mutanensu dake yin bincike da suka san abubuwan da su keyi. Yace su ba zasu sani ba amma Birtaniya da Amurka zasu sani. Yace maganar jakadan daidai take saboda idan ma akwai wadanda suke tunanen yin canjin gwamnati yanzu an nuna masu cewa an gane manufarsu.

Ambassador Suleman Dahiru yace sojojin dake zuwa wurin 'yan siyasa a bincikesu sosai.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG