Jakadiyar tace ta kai masa ziyarar ce ta bankwana saboda ta kammala wa'adinta a kasarsa.
Tace ziyarar ta zamo wajibi domin sun yi aiki kafada da kafada da duk bangarorin gwamnatin ta Kamaru kama daga 'yan majalisu zuwa na zartaswa da shugaban kasa.
Tace zasu cigaba da taimakawa dakarun kasar Kamaru wajen ganin sun murkushe 'yan kungiyar Boko Haram da suke haddasa rigingimu a kasashe daban daban da suka hada da ita kanta Kamaru.
Dangane da dangantaka tsakanin majalisar dattawan Faransa da na Kamaru, Jakadiya Robbinson sai tace majalisar Faransa na bukatar kara habbaka dankon zumunci da na Kamaru.
Dr. Suleiman na ma'aikatar harkokin wajen Kamaru yace shi a nasa ganin bai ga wani aiki na musamman da jakadiyar tayi ba a kasar Kamaru musamman akan matsalar da suke fuskanta yau da kullum da 'yan Boko Haram. Kasar Faransa tayi alkawarin magance matasalar 'yan ta'addan amma har yanzu babu abun da suka yi. Yace har yanzu Fransa ta barsu akan mulkin mallaka duk da wai ta tafi amma har yanzu tana mulkinsu.
Ga rahoton Garba Awal da karin bayani.