Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jani'an Amurka da Na Rasha Sun Tattauna Akan Syria


Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry da takwaransa Sergey Lavrov na kasar Rasha
Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry da takwaransa Sergey Lavrov na kasar Rasha

Amurka da Rasha dukansu suna kai hare hare cikin wasu sanssan kasar Syria kowannensu kuma da tashi manufar da a wani lokacin suna karo da juna.

Jami’an rundunar sojojin Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawarsu karo na uku don fayyace dokoki da ka’idojin sararin samaniyar Syria.

Domin samin daidaiton fahimtar dokokin salama wajen aiwatar da ayyukansu da nufin gujewa hatsarin karon battar da ba a yi niyya ba.

Ma’aikatar tsaron Amurka tace, an sami ci gaba a taron tattaunawar da ya gudana ta hanyar sadarwar bidiyo ta yanar gizo a jiya Laraba.

Wanda tattaunawar ta maida hankali ne kacokan a game da matakan kare lafiya ta wajen kaucewa arangama.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa, taron ya maida hankali wajen fidda daftarin matsayarsu a nan gaba.

Dukkan bangarorin kasashen biyu sun yarda da cewa, an yi tattaunawar bisa kwarewar aiki, sannan gab ake da cimma yarjejeniya.

XS
SM
MD
LG