Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Britaniya da Amurka Na Kyautata Zaton ISIS Ce Ta Kado Jirgin Fasinjan Rasha


Baraguzan jirgin da ya fadi
Baraguzan jirgin da ya fadi

Jami'an Amurka dana Britaniya suna gayawa kafofin yada labarai cewa "akwai kyakkyawar zaton" cewa bam ne ya haddasa faduwar jirgin fasinja na Rasha wanda yayi hadari a zirin Sinai makon jiya, ya halaka illahirin fasinjoji 224 da suke ciki.

Wani jami'in Amurka ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa,maganganu da aka saurara ya nuna cewa kungiyar ISIS ce take da alhakin tarwatsa jirgin.

Kwararru suna nazarin baraguzan jirgin domin gano ko akwai alamun ta'addanci. Wasu rahotanni sun ce bincike na kimiyya ya nuna kusoshi a jikin fasinjojin. Haka nan kwararrun sun gano akwatunan tattara bayabnai na jirgin guda biyu duka.

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin haddasa faduwar jirgin, sai dai bata nuna wani shaida ba da zai tabbatar da wannan ikirari da tayi.

Amma shugaban Masar Abdel Fattah el-Sissi, yayi watsi da ikirarin na ISIS da cewa "farfaganda ce" kawai da suke yi da niyyar nakasa tafarkin tsaro da daidaiton na Masar.

Wani masani kan harkokin gabas ta tsakiya a wata cibiya dake nan Washington DC, David Schenker, ya gayawa Muryar Amurka cewa " ba zai kasance abun mamaki ba " idan aka tabbatar da cewa kungiyar ISIS ce ta haddasa faduwar wannan jirgi.

XS
SM
MD
LG