Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Gwamnatin Colombia da Wakilan 'Yan Tawayen Kasar Sun Gana A Cuba


Shugaban Colombia da shugaban 'yan tawaye
Shugaban Colombia da shugaban 'yan tawaye

Jami'an gwamnatin Colombia sun gana jiya Talata a kasar Cuba, da wakililan 'yan juyin juya halin sojojin Colombia don tattaunawa kan yadda za a ceto yarjajjeniyar zaman lafiya daga wargajewa, to amma ba a san ko 'yan tawayen na da niyyar sake komawa kan teburin shawara ba ko a'a.

Bayan ga batun sake komawa kan teburin shawara da 'yan tawayen, Shugaban Colombia Manuel Santos zai kuma gana da tsohon Shugaban kasar Alvaro Uribe, wanda ya yi nasarar sasanta bangaren adawa da kungiyar ta FARC. Uribe ya gaya ma wani gidan rediyon Colombia cewa a shirye ya ke ya taimaka wajen cimma jituwa da kungiyar ta FARC da kuma kawo karshen yakin da kasar ta shafe shekaru 52 ta na gwabzawa.

Saura kiris masu kada kuri'a su amince da yarjajjeniyar zaman lafiyar da kashi 50.2% akasin 49.7%; wato da rinjayen kuri'u 54,000. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a game da zaben raba gardamar na ranar Lahadi ta nuna cewa za a amince da rinjayen daya zuwa biyu.

XS
SM
MD
LG