Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an Kiyaye Gabar Tekun Libya Sun Ceto Bakin Haure 350


Wani jirgin ruwan jami’an kiyaye gabar tekun Libya ya kwashe wasu bakin haure 350 a kan teku a jiya Laraba, bayan wata zazzafar arangama da wani jirgin ruwan Jamus mai shawagi kan teku wanda ka iya kai ga mutuwa.

Rahotannin sun ce babu wanda ya rasa ransa kuma an yi nasarar ceto bakin hauren a birnin dake gabar tekun Libya na Sabratha wanda a halin yanzu su na cikin koshin lafiya a birnin Tripoli.


Wani kakakin sojin ruwan Libya yace an cusa bakin hauren ne a wani karamin jirgin ruwan katako. A yayin da jirgin sojin Libyan ke kokarin kai gab akin hauren, sai ga wani jirgin Jamus mai shawagi kan teku ya kutsa inda jirgin Libyan yake. Wanda ya so ya janyo hadari.


Jirgin Jamus ya yi kokarin ficewa daga yankin tekun Libya, yana cewar mayar da bakin hauren zuwa Tripoli yana da hadarin gaske.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG