Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamian Sojojin Gbagbo Sun Yiwa Outtara Mubayia


Shugaba Alassane Ouattara a otel Golf tare da hafsan hafsoshin sojojin kasar Ivory Coast janar Philippe Mangou da kuma sauran jami'an sojoji.
Shugaba Alassane Ouattara a otel Golf tare da hafsan hafsoshin sojojin kasar Ivory Coast janar Philippe Mangou da kuma sauran jami'an sojoji.

Hafsan hafsoshin sojojin tsohon shugaba Laurent Gbagbo janar Philippe Mangou ya na umartar sojoji su koma ga aiki a karkashin sabuwar gwamnatin shugaba Alassane Ouattara.

Sojojin Faransa da na Ivory Coast ne ke yin sintiri a kan titunan birnin Abidjan, su na aikin farfado da tsaro a birnin bayan rikicin zaben da aka yi watanni hudu ana yi.

Hafsan hafsoshin tsohon shugaba Laurent Gbagbo, janar Philippe Mangou, ya na umartar sojoji su koma ga aiki a karkashin sabuwar gwamnatin shugaba Alassane Ouattara.

Janar Mangou ya ce dole ne sojoji su yi mubayi'a ga sabon shugaban su wanda ya ba su umarnin cewa su taimaka su tabbatar da tsaro a birnin Abidjan da kuma sauran sassan kasar Ivory Coast.

Shugaba Alassane Ouattara na yin musabaha da hafsan hafsoshin tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo, janar Philippe Mangou a otel Golf, helkwatar gwamnatin sabon shugaban kasar.
Shugaba Alassane Ouattara na yin musabaha da hafsan hafsoshin tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo, janar Philippe Mangou a otel Golf, helkwatar gwamnatin sabon shugaban kasar.

Da yawa daga cikin manyan jami'an sojojin Mr.Gbagbo sun yiwa Mr.Ouattara mubayi'a a jiya talata, kwana daya bayan da sojoji su ka cafke tsohon shugaban kasar a cikin wani al'amarin da ya kawo karshen jayayyar da ya yi ta yi da nufin dawwama a mulki.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Mr.Gbagbo da matar shi Simone dukan su , su na otel Golf a birnin Abidjan su na tsare a hannun Majalisar ta dinkin duniya.

Mr.Ouattara ya yi watsi da jita-jitar cewa wai za a kai Mr.Gbagbo kotun duniya ta birnin Hague. Ya ce ba za a wulakanta wadanda aka kama ba kuma za a girmama hakkokin su.

Ministan tsaron kasar Faransa Gerard Longuet ya fada a yau laraba cewa nan kusa Faransa za ta kwashe sojojin ta dari takwas daga cikin dubu daya da dari bakwai din da ke girke yanzu haka a kasar Ivory Coast.

A jiya talata birnin Abidjan ya yi fama da kwasar ganima jefi-jefi da kuma harbe-harbe da manyan bindigogi a lokacin da sojojin Ouattara ke kokarin kama matasa 'yan bangar Mr. Gbagbo, musamman ma shugaban su Charles Ble Goude.

XS
SM
MD
LG