Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaron Faransa na Rwanda Don Bincike Kan Kisan Kiyashin


Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ne da takwararsa ta Jamus Angela Markel.
Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ne da takwararsa ta Jamus Angela Markel.

Jami’an tsaron Faransa sun je Rwanda don su binciki ‘yan

Jami’an tsaron Faransa sun je Rwanda don su binciki ‘yan Rwanda da ke zaune a Faransa da ake zargin sun a da hannu a kisan kiyashin 1994.

Jean-Bosco Siboyintore, mai shugabantar sashen farauto madanda su ka gudu a ofishin masu gabatar da kara da ke Rwanda, ya gaya wa manema labarai cewa jami’an tsaron za su kasance a kasar na tsawon sati biyu, su yi binciken batutuwa da dama.

Jami’in y ace kasar Rwanda ta bayar da sammacin kama akalla ‘yan ruwanda 12 da ke zaune a Faransa.

Daya daga cikin wadanda ake zargin it ace Agathe Habyarimana, matar marigayi shugaba Juvenal Habyarimana. A na ganin kisan gillar da aka yi wa tsohon shugaban a watan Afiriluin 1994 shi ne ya haddasa kisan kiyashin da aka yi wa kimanin ‘yan Tutsi 800,000.

A na wannan binciken ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin Faransa da Rwanda ke kara inganta. Rwanda ta yanke huldar jakadanci da Faransa a 2006 bayan da wani alkalin Faransa ya zargi shugaba Paul Kagame da bayar da umurnin kashe Mr. Habyarimana.

XS
SM
MD
LG