Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyar CPR Ta Tsai Da Kassim Mukhtar Dan Takararta


Tambarin Jamhuriyar Nijar
Tambarin Jamhuriyar Nijar

Kamar yadda aka zata, duk da abin da wasu ke zargin tursasawa ce ta gwamnati, jam'iyyar adawa ta gwamnati ta tsai da Kassim Mukhtar a matsayin dan takararta

Babbar Jam’iyyar adawa a Janhuriyar Nijar, CPR Inganci ta yi babban taronta wato “Congre,” a birnin Damagaram, inda ta zabi jigonta Kassim Mukhtar a matsayin dan takararta na Shugaban kasa na zaben 2016.

Bayan taron, Kassim Mukhtar ya zanta da manema labarai ya shaida masu cewa tun bayan taron Maradi ne aka yanke shawarar tsai da shi dan takara. Y ace abin da ya sa aka tsai da shi dan takara shi ne ganin irin rawar da ya taka a matsayin Magajin Gari.

Alhaji Mukhtar ya yi takaicin abin da ya kira yawan ba da cin hanci da ake ta yi a kasar a maimakon a yi aikin gina kasa ko kyautata ma jama’a da irin wadannan kudaden. Yan a mai kira da aka kyautata bangaren shari’a don a yi adalci, sannan a kuma inganta tsaron kasa. Y ace bangern noma ma na bukatar a inganta sannan a samar ayyukan yi musamman ga matasa.

Ga Tamar Abari da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:12 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG