Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Democrat Ta Tabbatar Da Tsayar Da Hillary Clinton A Matsayin 'Yar Takara


Jam’iyyar Democrat ta tabbatar da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, a matsayin ‘yar takarar neman shugabancin Amurka karkashin tutar jam’iyyar, wanda hakan yasa ta zama mace ta farko da ta taba zama ‘yar takarar ‘daya daga cikin manyan jam’iyyun kasar, a yakin neman shugabancin Amurka.

A taron jam’iyyar na jiya Talata, Sanata Bernie Sanders, ya fadi cewa yana son a dakatar da kuri’un da za a jefa, a tabbatar da Hillary Clinton a matsayin ‘yar takarar jam’iyyar.

Wannan lamari ya banbanta da abinda Hillary tayi shekaru Takwas da suka gabata lokacin da tayi jawabin nuna goyon bayanta ga abokin karawarta na wancan lokacin Barack Obama.

Da yake yanzu an tabbatar da Hillary a matsayin ‘yar takarar jam’iyyar a hukumance, mijinta tsohon shugaban Amurka, Bill Clinton, yayi jawabi a taron na jiya inda yake nunawa Amurkawa dalilan da zai sa su zabi matarsa a babban zabe na watan Nuwamba, domin ta zamanto shugabar kasar Amurka ta 45 bayan shugaba Obama ya bar ofis cikin watan Janairun shekara mai zuwa.

XS
SM
MD
LG