Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar PDP Mai Mulkin Najeriya Ta Sha Kaye A Wasu Mazabun


Wani ma'aikacin zabe yana nuna takardar kuri'ar da aka soke saboda tawadda ta taba alamu har biyu a wata rumfar zabe a Abuja, asabar 9 Afrilu, 2011
Wani ma'aikacin zabe yana nuna takardar kuri'ar da aka soke saboda tawadda ta taba alamu har biyu a wata rumfar zabe a Abuja, asabar 9 Afrilu, 2011

Rahotanni na nuni da cewa jam'iyyun ACN da CPC su na kwace wasu kujerun jam'iyyar PDP a majalisun dokokin tarayya biyu

Sakamakon zabubbukan Majalisun Dokokin tarayya a Nijeriya na nuna cewa jam’iyyun adawa na yin galaba sosai kan jam’iyyar PDP mai mulki.

Jaridun Nijeriya sun labarto cewa Kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya, Dimeji Bankole, ya sha kashi a hannun dan takarar jam’iyyar adawa ta ACN.

Diyar tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo, ita ma dan takarar ACN ya lallasa ta.

Sakamakon ya nuna cewa jam’iyyar ACN na yin galaba a wurare da dama a kudu maso yamma, inda a nan yankin ne cibiyar cinakayyar Nijeriyar Nijeriya, Lagos, ta ke. Wata jam’iyyar kuma mai suna CPC na yin fice sosai a arewacin Nijeriya.

An gudanar da zaben na ranar Asabar ne bayan an dage sau biyu kuma duk ko da tayar da bama-baman da aka yi a biranen Maiduguri da Suleja.

Masu sa ido na kasa da kasa sun ce ga dukkannin alamu an kamanta adalci wajen gudanar da zabubbukan, to saidai an dan sami rudami sanadiyyar yawan jama’a.

Hukumar zaben Nijeriya na son ta sha bamban da tarihin zabubbukan baya, da tashe-tashen hankula da magudi su ka dabaibaye.

XS
SM
MD
LG