Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janar Babangida Mai Ritaya Yace A Maida Majalisun Dokokin Tarayya Na Wucin Gadi


Tsohon shugaban Mulkin Soja a Najeriya Janar Ibrahim Babangida.
Tsohon shugaban Mulkin Soja a Najeriya Janar Ibrahim Babangida.

Tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Babangida ya shawarci shugaba Goodluck Jonathan yayi wa tsarin mulki kaskwarima a maida majalisun dokoki na wucin gadi, domin a rage kashe kaudi.

Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bada shawarar a yi kwaskwarima ga tsarin mulki ta yadda majalisun dokokin tarayya zasu zama na wucin gadi.Ta wan nan hanya inji janar Babangid gwamnati zata rage kashe kudi da take cewa bata dasu ahalin yanzu.

Haka kuma Janar Babangida yayi magana kan wasu hanyoyin rage ayyuka da gwamnatin tarayya dake gudanar wa yanzu.

Janar Babangida ya bayyana haka ne a hira da yayi da sashen Hausa na Muriyar Amurka.

Saurari:

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG