Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janar Stanley McChrystal Yayi Murabus


Shugaba Barack Obama ya bayar da sanarwar amincewa da takardar murabus ta janar McChrystal a bayan da babban hafsan da mukarrabansa suka furta kalamun nuna raini ga manyan jami'an gwamnati.

Shugaba Barack Obama na Amurka ya amince da takardar murabus daga kan mukamin babban kwamandan sojojin Amurka a Afghanistan wadda Janar Stanley McChrystal ya mika.

Yau laraba a fadar White House shugaba Obama ya bayar da sanarwar murabus din ta Janar McChrystal a bayan da janar din da mukarrabansa suka furta kalamun nuna raini ko batunci kan manyan jami'an gwamnatin Obama a cikin wata mujalla.

Shugaban ya nada Janar David Petraeus, kwamandan Rundunar Sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya, a zaman wanda zai gaje mukamin Janar McChrystal, yana mai fadin cewa yin hakan zai kyale Amurka ta ci gaba da kokarin da take yi yanzu haka a yakin Afghanistan ba tare da ja-baya ba.

Mr. Obama yace duk da nauyin rashin jagoranci irin na Janar McChrystal, wannan shawara ita ce wadda ta fi dacewa ga tsaron kasa. Yace kalamun da McChrystal ya fada cikin wannan mujalla sun saba da matsayinsa na kwamandan dake jagorancin sojoji a bakin daga.

A cikin sanarwar da ya bayar a bayan da shugaban ya sanar da murabus dinsa, McChrystal ya ce ya mika takardar murabus ne a saboda kwadayin da yake yi na ganin Amurka ta samu nasarar ayyukan da take gudanarwa a Afghanistan.

McChrystal yace yana goyon bayan manufofin shugaba Obama a Afghanistan dari bisa dari.

XS
SM
MD
LG