Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janar Zai Iya Kawo Canji – inji Wammako


Dan takarar shugabancin kasa kuma tsohon shugaba Muhammadu Buhari kafin ya gabatar da kudurinsa a taron fidda gwani da APC tayi, Disamba 11, 2014.
Dan takarar shugabancin kasa kuma tsohon shugaba Muhammadu Buhari kafin ya gabatar da kudurinsa a taron fidda gwani da APC tayi, Disamba 11, 2014.

Gwamnan Jihar Sokoto, Aliyu Magatakarda Wammako ya bayyana zaben share fage na APC a matsayin Ikon Allah, a hirar da yayi da wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka, Hassan Umaru Tambuwal.

“Anyi adalci idan ka lura da abunda aka yi, domin an baiwa kowani dan takara dama ya bayyana abunda yake son yi, da yadda ya fahimci matsalolin kasarnan (Najeriya), da kuma abunda zaiyi idan ya samu shugabanci”, a cewar gwamnan na Sokoto.

Mr. Wammako ya cigaba da cewa “duk wanda ya san gaskiya, ya san cewa wannan zaben da aka yi, to akwai taimakon Allah a ciki, amma irin sanin da akayi wa Janar, mutane sun san cewa zai iya kawo canjin da ake bukata cikin yardar Allah.”

Gwamna Wammako yayi karin haske game da irin salon shugabanci da dan takarar Janar Buhari ya sani, da kuma abunda zai fuskanta a demokradiyyanci idan yayi nasara.

“Mulkin da yayi can da, na soja ne. Muka zo yanzu na siyasa ne, akwai ban-banci tsakanin mulkin soja da na siyasa. Mu da muka zabe shi, dole mu bashi goyon baya don ya samu nasara.”

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG