Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Japan Ta Ce An Yi Jinyar Biyu Daga Cikin Masu Aiki A Tashar Nukiliyar Da Ta Lalace


Hayaki kenan a tashar nukiliyar Fukushima da ta lalace
Hayaki kenan a tashar nukiliyar Fukushima da ta lalace

Hukumomi a Japan sun ce an yi jinyar ‘yan kwana-kwana biyu daga cikin masu kai dauki a tashar nukiliyar kasar da ta lalace saboda lahanin da tururin nukiliya ya yi wa kafafunsu bayan.

Hukumomi a Japan sun ce an yi jinyar biyu daga cikin masu kai dauki a tashar nukiliyar kasar da ta lalace saboda lahanin da tururin nukiliya ya yi wa kafafunsu bayan.

Babban Sakataren Majalisar zartaswar Japan ya fadi a yau Alhamis cewa ma’aikata uku sun harbu da tururin nukiliyar fiya da kima a yayin da su ke kyaran mafificin sanyaya tukunya ta uku a tashar nukiliyar ta Fukushima, wadda ake ganin ta fi hadari cikin dukkannin tukwane shida na tashar nukiliyar saboda rodin da ke dauke da man nukiliyar na kunshe da sinadarin plutonium mai wuyar sha’ani.

Yukio Edano ya ce mutane ukun na harhada kebur din wutar lantarki ne a dakin karkashin kasa na ginin da ke kunshe da tukunyar nukiliyar sai biyu daga cikinsu suka tsoma kafafunsu cikin gurbataccen ruwan da gubansa ya kai ga kafafunsu. Mai magana da yawun kamfanin da ke kula da tashar y ace an kai ma’aikata biyun wani asibitin da ked a kayan jinyar gubar nukiliya.

A yau Alhamis an cigaba da aiki a tashar, wace ke sace tururi mai guba tun bayan da maficin sanyaya ta ya lalace sanadiyyar mummunar girgizar kasa da ambaliyar ruwan tsunamin das u ka faru sati biyu das u ka gabata.

XS
SM
MD
LG