Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jared Loughner Ya Amsa Laifinsa A Gaban Kotu


Jared Loughner, mutumin da ya nemi kashe 'yar majalisar wakilan tarayya Gabrielle Giffords
Jared Loughner, mutumin da ya nemi kashe 'yar majalisar wakilan tarayya Gabrielle Giffords

Amsa laifin da Loughner yayi gaban kotu a Tucson, a Jihar Arizona, ta sa zai kaucewa fuskantar hukumcin kisa, sai daurin rai da rai kawai

Mutumin da ake zargi da harbe-harben da suka raunata wata 'yar majalisar wakilan tarayyar Amurka da kuma kashe mutane 6 cikin watan Janairun shekarar 2011 a Jihar Arizona, ya amsa laifinsa a gaban kotu.
Amsa laifin da Jared Lee Loughner yayi jiya talata a garin Tucson dake Jihar Arizona, ya ba shi damar kaucewa fuskantar hukumcin kisa a saboda wannan laifi da ya aikata. Ma'aikatar shari'a ta tarayya ta Amurka, ta ce a karkashin sharrudan amsa laifin nasa, za a yanke ma Loughner hukumcin daurin rai da rai har sau bakwai da zai yi daya bayan daya, sannan kuma da wani karin dauri na shekaru 140 a gidan kurkuku.
Lauyan gwamnatin tarayya, John Leonardo yace wannan yarjejeniya zata tabbatar da cewa "wanda ake tuhumar ya shafe tsawon rayuwarsa a cikin kurkuku ba tare da ahuwa ba."
Wadannan harbe-harben da yayi sun bazu a duniya a saboda Loughner yayi niyyar harbe 'yar majalisar dokokin Amurka, Gabrielle Giffords ne.
Wani alkali a Arizona ya yanke hukumci a bara cewa Loughner ba ya cikin hankalin da zai iya tsayawa gaban shari'a, a bayan da aka shafe makonni biyar likitocin mahaukata su na duba shi a asibiti. Amma a jiya talata, wani alkalin kotun tarayya ya yanke hukumcin cewa Loughner yana da cikakken hankali a yanzu da zai iya fahimtar irin tuhumar da ake yi masa.
XS
SM
MD
LG