Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jaridanci Da 'Yancin Jama'a


Mutane na sayan jaridu da mujallu. Wani sa'in akan samu takaddama kan abubuwan da jaridu kan wallafa.
Mutane na sayan jaridu da mujallu. Wani sa'in akan samu takaddama kan abubuwan da jaridu kan wallafa.

Wani mai fashin baki ya ce da muhimmancin a tabbatar da 'yancin mutum da kuma na jarida kafada da kafada

Wani dadadden dan jarida mai fashin baki kan al’mura kuma Editan jaridar Rariya da ke Abuja, mai suna Ashafa Manir Barkiya, ya bugi jaki ya kuma bugi taiki game da batun harin da aka kai gidan jaridar barkoncin nan ta Charlie Hebdo, dangane da zanen barkocin da ta kan yi kan Annabi Muhammad. A hirarsu da Aliyu Mustafan Sakkwato kan wannan batun Edita Barkiya ya ce, “Wannan mujalla ta Charlie Hebdo, kamar yadda kowa ya sani, ba wannan ne karon farko da ta yi zane na batanci ga Manzo Sallalahu alaihi wa sallam ba. Ba shakka abin da ya faru ga wannan gidan jarida abin takaici ne a ce an je an kashe su; to amma akwai abin da ya kamata dan adam, ko Musulmi ne ko Bayahude ko Kirista -- ko a wace kasa ya ke a duniya, ya duba. Na farko dole a yaba wa Faransa kasancewar ita ce kasa ta Yammacin Turai wadda ta fi bude kofarta ga dukkan Musulmi na Afrika musamman Afirka ta arewa da Magrib su sami wurin fakewa a matsayin hijira, ko don gudun talauci – su tafi can neman aiki ko wasu dalilai dabam.”

Ya ce kasashen Magrib da na Larabawa yawancinsu sun yi kaka gida a Faransa. Saboda haka “duk kasar da ta ba wasu baki wadanda ba mabiya addininta ba dole a yaba ma ta. To amma a matsayin su na ‘yan kasa, dole ka san cewa ko da wa ka ke zaune, ka na da ‘yancinka, shi ma ya na da ‘yancinsa kuma akwai hakki na mutunta bil’adama a duk inda ya ke. A Amurka har kungiyoyi ake da su wadanda ko wani zane ko kwarzane ka yi wa wani jaki ko kare ko doki, z aka ga an far ma ka bare dan adam.”

Ya ce a saninsa dai a ka’idar aikin jarida babu damar ka tozarta wani abin da wasu su ka dogara gas hi duniya wa lahari. Y ace idan mutum ya yi zane don ya bai wa mutane dariya sai ya kasance a duniya inda ka ke so a yi dariyar zanen da ka yi mutane sama da biliyan daya da rabi ba su yi dariya ba sai ma haushisu ka ji, to ya kamata kai kanka ka san cewa abin da ya yi ba daidai ba ne.

Jaridanci da 'Yancin Jama'a - 3'30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG