Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabin Donald Trump Bayan Lashe Zaben Amurka


ግጥም ኩዕሶ እግሪ ኤርትራውያን ሰሜን ኣሜሪካ ኣብ ሚንያፖሊስ
ግጥም ኩዕሶ እግሪ ኤርትራውያን ሰሜን ኣሜሪካ ኣብ ሚንያፖሊስ

Donald Trump shine ya zama zababben shugaban kasar Amurka.

Attajirin dan kasuwar nan da mutane masu yawa suka raina har wasu 'yan siyasa da kamfanonin yada labarai suke tsokana kusan baki daya lokacin kamfe dinsa, ya sami nasara mai ban mamaki ajiya Talata akan abokiyar karawarsa tsohuwar sakatariyar Harkokin wajen Amurka Hillary Clinton.

Trump kewaye da iyalansa da kuma manya manyan wadanda suka taimaka masa a wajen bikin murnar nasarar da ya samu a birnin New York, a yau Laraba ya fada cikin farin ciki cewa “ Nayi alkawari ga kowanne dan kasa cewa zan zama shugaban kowane BaAmurke”.

Shugaban Kasa Barack Obama ya yiwa Trump murnar samun nasarar da yayi ta tarho kuma ya gayyace shi zuwa White House a ranar Alhamis mai zuwa.

Sakataren yada labarai Josh Earnest yace “ Tabbatar da kyakykyawan mika mulki yana daya daga cikin abubuwa marasa muhimmanci da shugaban kasa ya bayyana a farkon wannan shekarar sannan haduwa da sabon zababban shugaba a matsayin mataki na gaba.

Ba’a taba tunanin samun nasara ga dantakarar da bai taba rike kujera ko da guda daya ba, da kuma yin kamfe ba kamar yadda aka saba ganiba a tarihin Amurka. Sannan ya kawo karshen kamfen da ya jawo rarrabuwar kai da za’a iya tunawa.

Trump dan jam’iyyar Republican, ya sami kuri’un masu zaben shugaban kasa da ake yiwa lakabi da electoral vote 288 a yayin da abokiyar karawarsa ta Democrat Hillary Clinton ta sami 215 kamar yadda sakamako ya nuna a yau Laraba.

XS
SM
MD
LG