Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Watanni ba a Samu Bullar Polio a Jihar Borno Ba


Kwamishinar kiwon lafiya ta jihar ta ce duk da tashin hankalin 'yan Boko Haram a jihar, ana samun ci gaba a harkokin kula da lafiyar jama'a.

Kwamishinar kiwon lafiya ta Jihar Borno, Dr. Salma Anas Kolo, ta ce an shafe watanni da dama ba a samu bullar cutar Polio, ko shan inna a cikin jihar ba.

Kwamishinar ta fadawa 'yan jarida cewa duk da tashin hankalin da ake fama da shi kusan kullum a jihar ta Borno, ana samun ci gaba a bangaren kiwon lafiyar jama'a.

Ta ce duk da irin wannan tashin hankalin, ana ci gaba da gudanar da ayyukan rigakafi a fadin jihar, yayin da dukkan cibiyoyin lafiya da asibitocin jihar su ma suke ci gaba da aiki a cewarta.

Kwamishinar ta klara da cewa gwamnatin jihar ta sayi motocin daukar marasa lafiya masu yawa wadanda ake amfani da su wajen gaggauta jigilar wadanda suka samu rauni zuwa asibiti domin ba su kulawar da ta kamata.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG